Bayan Shakaru Takwas, Za'a Rataye Sagir Wada, Wanda Ya Yi Gunduwa-Gunduwa da Kishiyar Mamarsa a Kano


Babbar Kotun jihar Kano mai zama a Sakatariyar Audo Bako, ta yanke wa wani mutumi, Sagiru Wada, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama shi da laifin kisan matar babansa. Legit ta wallafa.

Jaridar Daily Trust ta ce Alkalin Kotun mai shari'a Aisha Mahmud, ta yanke masa hukuncin ne bayan nazari kan dukkan batutuwan dake ƙunshe a cikin Kes ɗin.

Bayan dogon Nazarin, Alkalin tace ta kama Wada da laifin halaka matar babansa ta hanyar datsa ta gunduwa-gunduwa karkashin sashi na 221 na kundin dokokin Fenal Code, Kano.

Mai shari'a Aisha Mahmud tace ta gamsu da dukkan shaidun da aka gabatar a gaban Kotu, inda ta bayyana cewa bangaren masu kara sun tabbatar da aikata laifin ba bu tababa.

Yadda shari'ar ta gudana

Legit.ng Hausa ta gano cewa an gurfanar da Sagir Wada a gaban Kotu ne shekaru Takwas da suka gabata bisa tuhumar kashe kishiyar mahaifiyarsa, Zainab Dan-Azumi, da wuka.

Lauyan dake kare wanda ake zargi, Barista Rabiu Abubakar, ya shaida wa Kotu cewa Sagir Wada na fama da taɓin hankali amma Kotun ta yi fatali da zancen saboda shaidun da aka gabatar.

Haka zalika lauyan mai ƙara, Barista Tijjani Ibrahim yace Kotu ta nazarci yadda Kes din ke tafiya cikin nutsuwa kuma babu wata hujja da ta tabbatar wanda ake zargi na da tabin hankali.

A halin yanzu, lauyan dake kare wanda ake tuhuma ya ce zasu yi nazari kan hukuncin da Kotu ta yanke kuma su ɗauki mataki na gaba.

A kwanakin baya kunce cewa wata sabuwar matsala ta haddasa ɗage shari'ar kisan Ummita, budurwa yar Kano da wani Ɗan China ya kashe.

Lamarin dai ya kai ga tiƙasata Kotu ta sanar da ɗage zaman zuwa wata na gaba don shawo kan komai.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN