Babbar magana: 'Yan kwamitin yaki da 'yan daba sun rusa ofishin kamfen APC a jihar APC a Arewa


Gusau, jihar Zamfara - Kwamitin yaki da 'yan daba a jihar Zamfara ta jaddada manufarsa na kakkabe jihar daga 'yan daba da sauran masu tada hankulan jama'a, PM News ta ruwaito. Legit.ng ta wallafa.

Bello Bakyasuwa, Shugaban kwamitin, ya ba da tabbacin nan ne a wata tattaunawa da 'yan jarida a birnin Gusau na jihar a ranar Lahadi 11 ga watan Disamba.

Ya bayyana hakan ne jim kadan bayan da kwamitin ya rusa wani ofishin kemfen na APC mai mulkin jihar, tare da cewa ana zargin matasan da ke wurin 'yan daba ne da ke amfani da ofishin a matsayin mafaka.

Dalilin da yasa kwamitin ya rusa ofishin APC

Shugaban ya ce mutanen da ke zama a ofishin 'yan ta'adda ne da mutanen banza da kwata-kwata basu cancanci samun mafaka ba a cikin al'umma saboda barnar da suke aikatawa.

A cewarsa:

"Bisa bayanan sirri da kwamiti na ya samu kan mutanen da ke zama ofishin yakin neman zaben jam'iyyar mun gano suna fakewa domin aikata munanan ayyukansu na ta'addanci da sunan kamfen.

"Mun ma gano wasu kayan sakawa na mata yayin da muka runtuma kame a ofishin."

A wani rahoton TheCable, an ce 'yan daban na amfani da ofishin a matsayin wurin siyar da ababen hawa na sata.

Manufar kafa wannan kwmaitin ba sani ba sabo

Ya ce manufar kwmaitin shine tabbatar da zabe mai ma'ana da babu rikice-rikicen 'yan daba a fadin jihar a 2023.

Ya kuma gargadi jam'iyyun siyasa da 'yan siyasa da su guji daukar matasa suna daura su kan turbar dabanci, inda yace hakan na jawo rikici a lokutan zabe.

Gwamna Matawalle ne ya kirkiri wannan kwamiti domin yaki da ayyukan ta'addanci da dabancin siyasa ba tare da la'akari da jam'iyya ba a wata doka da ya samar.

A baya wasu 'yan daba suka lakadawa shugaban 'yan jaridar jihar ta Zamfara duka, lamarin da ya jawo cece-kuce a jihar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN