Alkali ya rataye kansa a coci bayan ya kashe matarsa ​​tare da yi wa gawarta fyade a gaban ‘ya’yansu

Alkali ya rataye kansa a coci bayan ya kashe matarsa ​​tare da yi wa gawarta fyade a gaban ‘ya’yansu


Wani Alkalin kasar Zimbabwe da ‘yan sanda suka bayyana cewa suna neman sa saboda kisan gilla da aka yi wa matarsa ​​ya kashe kansa a wata coci. Shafin isyaku.com ya samo.

Alkalin da ya rasu a yanzu Evans Zinzombe, mai shekaru 36, ya kasance yana gudu ne daga hannun ‘yan sanda bayan da ya kashe matarsa, Pholomina Mabika, mai shekaru 32, a ranar Laraba, 7 ga watan Disamba.

An ruwaito cewa ya shake Phelomina har lahira da hannunsa sannan ya ci gaba da yi wa gawarta fyade a gaban ‘ya’yansu;  'yar shekara 12 da kuma dan shekara 7.

Mai magana da yawun 'yan sanda, mataimakin kwamishinan Paul Nyathi wanda ya bayyana cewa ana neman Alkalin ya ce;

“Rundunar ‘yan sandan jamhuriyar Zimbabwe na neman bayanan da ka iya kai ga kama Alkali Evans Zinzombe (36), wanda ake nemansa da laifin kisan kai wanda ya faru a ranar 07 ga Disamba 2022 a wani gida a Cowdray Park a Bulawayo.

“Wanda ake zargin ya kutsa cikin dakin da matarsa ​​Pholomina Mabika ‘yar shekara 32, ‘yarsa (12) da kuma dansa (7) kafin ya shake ta har lahira.

“An rahoto cewa wanda ake zargin da matar sa na fama da rikicin aure wanda ya tilasta musu kwanciya a dakuna daban-daban.

“Bayan kisan gillar da aka yi, wanda ake zargin ya ci gaba da lalata da gawar a idon ‘ya’yansa.

“Yaran sun kwana tare da gawar kafin a kai rahoton wajen ‘yan sanda da safe.

Daga nan ne aka gano gawar Alkali Evans Zinzombe a rataye a rufin wani coci a unguwar Cowdray Park na Bulawayo.

Da take tabbatar da mutuwarsa, rundunar ‘yan sandan ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar;

"An tsinci gawarsa rataye ne a jikin rufin karfe a wani coci da ke Cowdray Park."

‘Yan sandan kuma suna daukar mutuwarsa a matsayin kashe kansa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN