Yar uwar babban Alkalin jiha ta gurfana a gaban Kotun Majistare bisa zargin cin zarafin mijinta

Yar uwar babban Alkalin jiha ta gurfana a gaban Kotun Majistare bisa zargin cin zarafin mijinta

Wata mata mai suna Hameedat Ajadi, a ranar Talatar da ta gabata an tsare ta a gaban wata kotun Majistare bisa zarginta da cin zarafin mijinta mai suna Mista Abdul-Hammed Oladipupo. NAN ta ruwaito.

Oladipupo ya shigar da karar kai tsaye na cin zarafi, barna da hargitsin jama’a kan tsohuwar matarsa, Ajadi, wacce aka ce ‘yar uwar Babban Alkalin Jihar Kwara ce.

Ya yi zargin cewa wanda ake tuhumar ta tuka mota da gangan kuma ta yi kokarin bugunsa.

Ya kuma yi zargin cewa ta buge shi da dutse.

Lauyan da ke ba Wanda aka yi kara kariya, Misis N. T. Obalowu, ta bukaci da cewa tunda bangarorin sun kasance mata da miji, to kotu ta bari a saurari maganar a zauren alkalai.

Ta kuma bukaci wanda ya shigar da karar ya shigar da karar da Lauyan da zai tsaya masa, inda ta ce ya sabawa ka’idar kotu idan mai karar ya karanta kokensa a gaban kotu da kansa.

Ta bukaci da a dage shari’ar ga wanda ya shigar da karan domin ya daidaita gidansa da kuma samun Lauyan da zai tsaya masa a kotu.

Amma  Oladipupo ya ki amincewa da Ć™addamarwa.

Babban Alkalin Kotun, Ibrahim Dasuki, ya ce kotun ba za ta amince da irin wannan bukata ba saboda sarkakiyar da kuma tarihin shari’ar.

Dasuki ya yanke hukuncin ne a kan bukatar Lauyan wanda ake kara, inda ya ce ya saba wa ka’idojin kotu idan mai korafi ya karanta da kansa ba tare da Lauya ba.

Alkalin kotun, ya umarci Oladipupo da ya samu Lauya da zai tsaya masa domin a fara shari’ar yadda ya kamata.

Don haka ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 11 ga Disamba.

Sai dai ya umarci Lauyan ya gabatar da wanda ake zargin a ranar da za a sake zaman kotu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN