‘Yan bindiga sun kashe manoma 12 tare da raunata wasu uku a kauyen Kaduna saboda kin biyan harajin amfanin gona.

A ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba, ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Rafin Sarki dake karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, inda suka kashe mutane 12 tare da raunata wasu uku.

Wani dan siyasa a yankin, Sambokhan Giwa, wanda ya tabbatar wa jaridar Sun da faruwar al’amarin a ranar Juma’a, ya ce an samu matsala ne a lokacin da ‘yan bindiga suka bukaci a biya su haraji daga manoman da suke girbin amfanin gonakinsu.

A cewarsa, manoman sun yi turjiya lamarin da ya harzuka ‘yan bindigar da ke dauke da makamai inda a lokacin da kura ta lafa, manoma 12 ne suka mutu sannan wasu uku suka jikkata.

“Gaskiya ne, sun kai hari wani kauye da ake kira Rafin Sarki ba a garin Giwa ba, a karamar hukumar Giwa, sun kashe mutum 12 tare da raunata uku,” inji shi.

“Mutanen yankin suna kwashe amfanin gonakinsu ne ‘yan fashin suka zo karbar kudi a wurinsu domin su ‘bar’ su gama aikin noma, amma manoman sun ki ba su kudaden da suka nema, daga nan ne abin ya far." in ji Giwa.

Ya kuma kara da cewa mutane ukun da suka tsira daga harin na samun kulawa a wani asibiti da ba a bayyana ba, yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda harin ya rutsa da su.

Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, ya ce an kuma kashe wasu mutane hudu a harin da ‘yan bindiga suka kai a kananan hukumomin Birnin Gwari da Kajuru na jihar. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN