Shugabannin Hukumomin Tsaro na Jihar Kebbi sun gana a ranar Talata 22/11/2022, a dakin taro da ke hedkwatar rundunar ‘yan sandan jihar, a garin Birnin Kebbi, inda dabarun inganta gine-ginen tsaro a jihar, da kuma tabbatar da daidaiton tsarin tsaro ga duk masu son siyasa na daga cikin abin da aka tattauna.
Hakan na da nufin samar da yanayi mai kyau ga al’ummar jihar Kebbi su ci gaba da gudanar da sana’o’insu na halal ba tare da tsoro ko tsangwama ba.