Jiragen yaki sun kassara karfin Turji, sun yi kaca-kaca da maboyar mai kawo masa makamai


A kokari da suke na yakar ta'addanci a fadin kasar, jirgin yakin rundunar sojojin sama ya yi luguden wuta a mabuyar kasurgumin mai safarar makamai, Mallam Ila a kauyen Manawa da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara. Legit.ng ta ruwaito.

Wani jami'in tsaro ya fadama PRNigeria cewa mai safarar makaman shine babban mai kaiwa kasurgumin dan ta'adda Bello Turji muggan makamai a Zamfara.

Ya ce:

"Jirgin yakin NAF karkashin Operation Hadarin Daji ya kai wani samame kan gidan Mallam Ila a yammacin ranar 18 ga watan Nuwamban 2022.

Mallam Ila shine ainahin wanda aka so farmaka saboda kusancinsa da hulda da yake yi da Bello Turji da Dan Bokoyo. Mayakansu sune suka kai hare-hare a karamar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara da kuma wasu yankuna na jihohin Kaduna, Neja, Kebbi da Sokoto.

"Bayan samamen da aka kai wajen an lura da fashewar abubuwa da dunkule wuta wanda ke nuni ga akwai abubuwan fashewa boye a wajen. An murkushe wasu yan ta'adda yayin harin."

Wata majiya ta kuma sanar da PRNigeria cewa Mallam Ila ya tsallake rijiya da baya amma ya ji munanan rauni·

Da aka tuntube shi, kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da samamen sannan ya jaddada cewa ayyukan sojoji na ci gaba da kawar da yan bindiga da yan ta'adda da dama a jihohin.

"NAF da sauran hukumomin tsaro na a kan gabar ganin an zo karshen kokarin da ake na yaki da ta'addanci.

"Muna kira ga yan Najeriya da su ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro da bayanai kan ayyukan miyagu domin matsalar tsaro da ake fama da shi a yanzu yana bukatar kowa ya shiga ayi da shi."

An kuma kama wasu mutane da ake zargi da buga kudaden jabu duk dai a jihar ta Kebbi.

'Yan sanda na ci gaba da bincike don gano yadda lamuran suka gudana da kuma yiwuwar daukar mataki na gaba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN