Akalla mutane 74 ne aka kwantar a asibiti yayin da motoci sama da 100 suka barnata yayin da wasu ‘yan bangar siyasa suka yi arangama a lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya je Maiduguri domin gudanar da yakin neman zabe. Vanguard ta ruwaito.
Kakakin jam’iyyar PDP, Dino Melaye ya bayyana hakan yayin taron gangamin jam’iyyar a Maiduguri.
Ya yi nuni da wani mutum da ke zargin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kokarin hana yakin neman zabe a jihar ta hanyar tura ‘yan daba su kai musu hari.
Ya ce, “Sun tura ‘yan barandansu ne suka kai wa ayarin motocinmu hari da duwatsu, sanduna, adduna yayin da muka fito daga fadar Shehu domin zuwa dandalin Ramat, duk a kokarinsu na hana taron mu.” Dino yace.
Ya koka da cewa “an jibge ‘yan daba a wurare da dama don kai wa magoya bayanmu hari. Amma muna so mu tabbatar musu cewa babu wanda zai iya hana mu.”
A kasa ga bidiyon yadda motocin da aka kai wa harin ke barin wurin:
Thugs attack Atiku's Convoy in Maiduguri, 74 hospitalised
— Vanguard Newspapers (@vanguardngrnews) November 9, 2022
Credit: Twitter // Ait_Online pic.twitter.com/2e9kvV7PwJ