An kama wata mata da ke rike da fure kan harin bam a Istanbul


Yan sanda sun kama wata da ake zargin yar kunar bakin wake ne bayan da wani bam ya kashe mutane shida, ciki har da wata yarinya da mahaifinta a Istanbul. Jaridar vanguard ta ruwaito.

Hotunan CCTV na baya sun nuna wata mata da ake zargin tana gudu, rike da jajayen fure na wasu lokuta kafin wani bom ya fashe a kan titin sayayya, ya raunata akalla wasu 81 a yammacin Lahadi.

Hotuna masu ban tsoro sun nuna gawarwakin da sika bazu a kan titin Istiklal, babban titin siyayya na Istanbul kusa da dandalin Taksim.

Tun da farko, Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya Süleyman Soylu ya ce ana tsare da wanda ake zargi.

"Matar da ake zargin ta tayar da bam din tana tsare a babbar ma'aikatar tsaro, kamar yadda ya shaida wa TRT Haber.

Mista Soylu ya ce yana zargin cewa bam din na kungiyar 'yan awaren Kurdawa ce ta PKK inda ya sha alwashin mayar da martani mai tsauri.

Ya ce: "Waɗanda suka jawo mana wannan zafin za su iya ƙara jin zafi."

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Tun da farko, mataimakin shugaban kasar Turkiyya Fuat Oktay ya ce: "Mun yi imanin cewa harin ta'addanci ne da wani maharin da muke dauka a matsayin mace, ya tayar da bam."

An bayar da rahoton cewa Hotunan CCTV sun nuna wata mata a zaune a kan benci na tsawon mintuna 45 kuma tana barin wata jaka jim kadan kafin fashewar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN