Yadda wani amini ya yaudari abokinsa ya saki matarsa shi kuma ya aureta sati guda da saki tana cikin Iddah a jihar Kebbi (Bidiyo)
Muhammad Wantu Badariya |
Ana zargin wani mutum mai suna Usman Muhammad Gwadangaji ya yaudari amininsa mai suna Muhammadu Wantu Badariya ya saki matarsa shi mai suna Fatima Abubakar kuma sai ya zagaya ya aure ta a jihar Kebbi.
Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa Muhammadu Wantu, ya shigar da kara ranar 7/10/2022 a Kotun shari'ar Musulunci da ke gangaren Takalau a garin Birnin kebbi yana rokon Kotu ta bi masa hakkinsa bisa yaudara da ya ce abokinsa ya yi masa.
Majiyarmu ta shaida mana cewa Muhammadu Wantu yana zargin cewa amininsa Usman Muhammed Gwadangaji, ya yaudare shi ya sa ya saki matarshi cewa idan ya yi haka zai bashi diyar yayanshi don ya aureta. Sai dai bayan Muhammadu Wantu ya saki matarshi ranar 23/9/2022, sai ya ki bashi shi auren diyarshi da ya yi masa alkawarin cewa zai sa a bashi aurenta. Bayan hana shi auren yarinyar, ranar 30/9/2022 sai Usman Muhammad ya zagaya ya auri Fatima Abubakar matar da shi abokinsa Muhammadu Wantu ya saki.
Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa wannan lamari ya faru ne mako daya bayan Muhammadu Wantu ya saki matarshi, Kuma tana cikin Iddah, amma Usman Muhammad ya je aka daura masa aure da tsohuwar matar abokinsa Muhammadu.
Majiyarmu ta shaida mana cewa Dan sanda mai gabatar da kara a madadin Kwamishinan yan sandan jihar Kebbi, bayan karanto zargi da ake yi wa Usman Muhammad da Fatima Abubakar ya ce ana zarginsu ne da laifin hada baki da cutarwa. Kotu ta tasa keyar Muhammadu da Fatima zuwa Kurkuku har tsawon mako daya kasancewa ranar da Kotu za ta sake zama domin ci gaba da shari'arsu.
Kazalika, Kotu ta yi umarnin a kamo Waliyin Fatima da ya bayar da autenta mai suna Abubakar Gwadangaji wanda bayani suka nuna cewa yayanta ne, da kuma Limamin da ya daura auren domin a gabatar da su gaban Kotu lokacin zamanta na gaba.
Latsa kasa ka kalli bidiyon yadda ta faru: