Wata mata mai suna Nafisa ta haifi 'ya'ya hudu ranar Juma'a 7/10/2022 a babban asibiti (general hospital) da ke karamar hukumar Koko besse a jihar kebbi.
Injiniya Abdullahi Ibrahim koko ya ambato cewa matar tana aure a garin Tulunbude Dake karamar hukuma ta Koko besse.
Jama'a na ci gaba da sa albarka a shafukan sada zumunta yayin da wata majiya ta ce jariran da mahaifiyarsu na nan lafiya.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI