Tsohon Saurayi ya aike wa Ango tsaffin hotunan Amaryarsa kafin ta tuba, aure ya mutu

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kafin ta tuba, aure ya mutu


Aure ya mutu a daren farko yayinda ake tsakiyar shagalin biki lokacin da Ango ya samu sakon hotunan Amaryarsa na irin lalatan da tayi a shekarun baya kafin su hadu.

Shafin LISA ya ruwaito cewa Angon ya samu wasika tattare da katin Memory da wani ya turo yana zargin Amaryar da kasance mutuniyar banza.

Hakan ya sa Angon ya hanzarta wajen kallon abinda ke cikin Memorin.

Ya shige cikin daki shi kadai don gani.

Ango ya shiga daki inda ya gano wani tsohon saurayinta ne ya aiko da sakon cike da hotunansu na da suna badala.

Wannan abu bai yi wa Angon dadi ba kuma take ya yanke shawarar kawo karshen shagalin da ake yi.

Kai tsaye Angon ya danna mata saki.

Daga baya Amaryar ta bayyana cewa lallai sun yi soyayya da tsohon saurayin amma daga baya suka fahimci cewa basu dace da juna ba. Sai ta yanke shawarar watsi da shi tunda iyayenta sun sama mata sabon saurayin da ya dace da ita.

Tsohon Saurayin ya bukaci ta ziyarcesa ana gab da aure

Ta kara da cewa tsohon saurayin ya bukaci ta kawo ziyara gidansa ana sauran yan kwanaki da aure amma tayi banza da shi.

Ta ce ba ta son ta sake maimaita irin kura-kuran da tayi a baya saboda tana son fara sabuwar rayuwa da mijinta.

Ashe wannan abu bai yiwa tsohon saurayin dadi ba inda ya fara dura mata ashariya kuma yayi alkawarin tona mata asiri.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN