Da dumi-dumi: Wani Safeton dan sanda ya harbe abokin aikinsa har lahira a wata zazzafar muhawara kuma ya gudu da bindiga AK47, duba yadda ta faru


Wani Sufeto na ‘yan sanda a jihar Abia ya mutu sakamakon harbin da abokin aikinsa wanda kuma shi Inspector ne, a yayin wata hatsaniya mai zafi a Umuahia, babban birnin jihar.

Dukkan ‘yan sandan biyu an ce suna tare da dan majalisar dokokin jihar Abia mai wakiltar mazabar Isiala Ngwa ta Arewa, Hon. Ginger Onwusibe.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Geoffrey Ogbonna, ya ce wanda aka kashe, Insifekta Ugwor Samuel, abokin aikin sa, Insifekta Atule Benedict ne ya harbe shi har lahira, dukkansu daga SPU base 15, jihar Anambra, amma wanda ke da alaka da Hon. Onwusibe. An tattaro cewa harbe-harbe har lahira ya biyo bayan wata hatsaniya tsakanin ‘yan sandan biyu kan wata matsala da ba a bayyana ba.

Wata majiya ta bayyana cewa, bayan faruwar lamarin, yunkurin kwance bindigar sifeton ‘yan sandan da aka ce ya yi kaca-kaca da shi, ya ci tura. Majiyar ta kara da cewa wanda ake zargin ya tsere da bindigar AK-47 zuwa wani wuri da ba a san inda yake ba, amma daga baya ya mika kan sa ga SCID Umuahia, inda ake tsare da shi.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa yanzu haka dan sandan da ya aikata laifin yana tsare yayin da aka ajiye gawar marigayin a dakin ajiyar gawa. Ya ce hukumar CID Umuahia na jihar tana bincike kan lamarin.

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE