Confidence Man: Abubuwan fallasa takwas da aka rubuta kan rayuwar Donald Trump


Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya kusa korar 'yarsa, kuma lokaci-lokaci yana watsa takardun hukuma a cikin shadda. BBC Hausa ya ruwaito.

Wadannan bayanan fallasar da kuma karin wasu batutuwa na cikin abubuwan bankada da Maggie Haberman, 'yar jaridar New York Times ta wallafa a cikin wani littafinta da ake matukar sa ran fitowarsa mai suna Confidence Man, wanda ya fito kasuwa yau Talata.

Littafin ya bi diddigin rayuwar Mista Trump ne daga lokacin da yake matsayin dan kasuwa a birnin New York zuwa ga rayuwarsa bayan zama shugaban kasa.

An tattara bayanan ne daga jerin tattaunawa da majiyoyi fiye da 200, ciki har da tsoffin mataimaka na musamman da kuma wasu hirarraki guda uku da shi kansa Trump ya yi.

Tsohon shugaban kasar ya soki lamirin marubuciyar inda ya rubuta a kafar sada zumuntarsa cewa littafin na kunshe da "kirkirarrun labarai masu yawa ba tare da kokarin fayyace gaskiyar al'amura ba ko kadan".

Nan ga takwas a cikin manyan abubuwan fallasa na littafin Confidence Man:

1) Trump ya so ya kori Ivanka da Jared Kushner

Yayin wani taro da Shugaban Ma'aikata na wancan lokaci John Kelly da mai ba da shawara a fadar White House Don McGahn, Maggie Haberman ta rubuta cewa Mista Trump ya kusa wallafa cewa 'yarsa, Ivanka, da surukinsa Jared Kushner - dukkansu manyan mashawarta na musamman a White House - sun bar mukamansu.

John Kelly ne ya dakatar da shi, bayan ya shawarce shi cewa ya yi magana da Ivanka da Mista Kushner kafin ya rubuta sakon a Tiwita.

Mista Trump dai bai taba yi musu magana game da lamarin ba, kuma sun ci gaba da kasancewa mashawarta na musamman a fadar White House har zuwa karshen gwamnatinsa.

Littafin ya kuma yi bankadar cewa a-kai-a-kai Mista Trump yana yi wa surukinsa kaca-kaca kuma a wani lokaci ma ya taba cewa Kushner "yana yin abubuwa kamar karamin yaro" bayan ya saurari wani jawabin da ya gabatar a bainar jama'a a 2017.

Mista Trump ya musanta cewa ya taba tunanin ya kori Ivanka da mijinta daga aiki. "Tatsuniya ce tsagwaro. Ban taba tunanin haka ba," in ji shi.

2) Trump ya yi tunanin yin luguden bama-bamai kan cibiyoyin sarrafa miyagun kwayoyi na Mexico

Maggie Haberman ta wallafa cewa Mista Trump ya yi tunanin kai hare-haren bam kan cibiyoyin sarrafa miyagun kwayoyi na Mexico a karo da dama - wani lamari da ya kada hantar tsohon Sakataren Tsaron Amurka Mark Esper.

Tunanin ya zo ne sakamakon wata tattaunawa da Mista Trump ya yi da Brett Giroir, wani jami'in kula da lafiyar al'umma da kuma wani sojan ruwa mai mukamin admiral.

Mista Giroir ya shiga babban ofishin shugaban kasa sanye da tufafin aiki - kamar yadda al'ada ta tanada inda ya fada wa Trump cewa ya kamata a san yadda za a yi da cibiyoyin samar da haramtattun kwayoyi na Mexico saboda a kawo karshen haramtattun ayyukan da ake kawowa ta tsallaken iyaka.

Sai dai ya yi kuskuren daukar Mista Giroir a matsayin wani jami'in soja, inda Trump ya ba da shawarar yin luguden bam a kan cibiyoyin hada kwaya. Fadar White House a matsayin martani ta nemi Mista Giroir ya daina sanya tufafin aikinsa.

3) Trump ya ji tsoron mutuwa sanadin cutar korona

Lokacin da Mista Trump ya kamu cutar korona a watan Oktoban 2020, abubuwa sun tabarbare a fadar White House, inda ya rika tsoron mutuwa.

A wani lokaci, mataimakin shugaban ma'aikatansa, Tony Ornato, ya yi gargadin cewa idan lafiyarsa ta ci gaba da tabarbarewa sai dai ya shirya tsare-tsaren tabbatar da ganin gwamnati ta ci gaba da aiki.

Wannan tsoro ya ci gaba da wanzuwa duk da kokari a karo da dama na ganin Trump ya rage barnar wannan annoba, daidai lokacin da yake bayyana damuwa cewa kwayar cutar tana dakushe kima da tagomashinsa a siyasance.

Maggie Haberman ta wallafa cewa tsohon shugaban ya nemi mataimakansa na musamman da ke kewaye da shi su cire takunkumansu kuma ya shawarci gwamnan New York na wancan lokaci Andrew Cuomo ya daina magana game da kwayar cutar a talbijin."Kada ka mai da cibi ya zama kari," Mista Trump ya fada wa Mista Cuomo, a cewar littafin. "Za ka mai da abin ya zama wata matsala."

4) Da yake ganawa da firaministar Birtaniya Trump ya yi maganar gidansa

Littafin Maggie Haberman ya yi bayani dalla-dalla game da ganawa da yawa tsakanin Mista Trump da shugabannin kasashen duniya.

Misali, a ganawarsa ta farko da firaministar Birtaniya Theresa May, Mista Trump ya yi bayani game da zubar da ciki inda ya ce "wasu suna goyon bayan rayuwa, wasu kuma suna goyon bayan zabi.

Yanzu a ce wasu dabbobi masu dabbare-dabbaren tatu su yi wa 'yarki fyade kumata samu ciki?"Daga nan sai ya canza batun da wata hira kan Arewacin Ireland don tattaunawa kan yadda za a hana wani kamfanin sarrafa iska daga kafa cibiyarsa a kusa da gidansa.

5) Trump ya nemi Giuliani ya "yi duk abin da zai iya" ya canza sakamakon zaben 2020

Lokacin da ta bayyana cewa Mista Trump ba zai yi nasara a zaben 2020 saboda Shugaba Joe Biden ya sha gabansa, ya yi kira ga tsohon magajin birnin New York da lauyansa Rudy Giuliani.

"To, Rudy, wuka da nama suna hannunka. Ka bazama, ka yi duk abin da kake so. Ban damu ba," Mista Trump ya ce bayan wasu lauyoyi sun ki yin abin da ya ce a yunkurinsa na kifar da sakamakon zaben.

"Lauyoyina ba su da kyau," ya fada wa Mista Giuliani, a cewar littafin. Lokaci zuwa lokaci kuma yana caccakar lauyan fadar White House Pat Cipollone.

Littafin ya yi bankadar cewa a lokacin, Mista Trump ya fi haba-haba da tatsuniyoyin kitsa makarkashiya kuma ya nemi lauyoyi da cewa masu ba shi shawara sun shiga rudani.

6) Trump ya samo hujjar kin biyan haraji a cikin jirgin sama

A cikin jirgin sama lokacin da yake yakin neman zaben 2016, Corey Lewandowski, manajan yakin neman zaben Trump da sakatariyar yada labaransa Hope Hicks sun nemi ya yi jawabi kan kiyawarsa ta sakin bayanin dukiyar da zai biyawa haraji - wani batu da suke gani a matsayin wata matsala ga yunkurin cin zaben Donald Trump.

Maggie Haberman ta rubuta cewa Mista Trump ya mai da martani, inda ya jingina da kujera kafin ya gurza yatsu bayan wani tunani bagatatan ya zo masa: "To, kun san cewa ana binciken kudina don tantance haraje-harajena, A ko da yaushe dukiyata tana fuskantar binciken kudi," he said."

To abin da nake nufi shi ne, kawai zan ce ne, 'Zan fitar da bayanan bayan an kammala binciken kudin. 'Saboda ba za a taba gama kididdige dukiyata ba.

"Tun Richard Nixon, duk shugaban Amurka bisa radin kai suna fitar da bayanan dukiyar da suka biyawa haraji. A 2020 wani binciken jaridar New York Times ya bankado cewa Mista Trump ya biya $750 (N547,500) a matsayin harajin kudin shigarsa ga asusun tarayya a shekarar da ya zama shugaban kasa.

7) Trump ya rika watsa takardun hukuma a masan fadar White House

Lokacin da Mista Trump yake ofis, ma'aikatan fadar White House lokaci-lokaci sun rika gano yadda takardu masu dauke da bayanai ke toshe masai, kuma an yi imani cewa shi ne yake watsa takardun hukuma a ciki.

An kuma yi zargin yana yaga takardun hukuma, abin da saba da dokar ajiye bayanan shugaban kasa - wata doka ce da ta zayyana cewa takardun da shugaban kasa ya rubuta ko ya karba, kadarori ne na gwamnatin Amurka kuma Hukumar kula da Kayan tarihin Amurka ce za ta ajiye su da zarar shugaban kasa ya kammala wa'adinsa.

An bankado wadannan bayanai ne ana tsakiyar zarge-zarge game da batan takardu daga fadar White House a zamanin mulkin Trump wadanda suka kamata a kai wa Hukumar kula da Kayan tarihi ta Kasa.

Mista Trump yana kuma fuskantar wani binciken aikata babban laifi daga Ma'aikatar Shari'ah saboda ajiye takardun bayanan gwamnati a gidansa na Mar-a-Lago da ke Florida bayan ya bar ofis.

8) Trump ya dauka cewa ma'aikata daga tsirarun kabilu masu kawo abinci ne

A wani babban taron 'ya'yan ja'iyya jim kadan bayan kaddamar da shi matsayin shugaban kasa a 2017, Maggie Haberman ta rubuta cewa Trump ya umarci rukunin tsirarun kabilun 'yan jam'iyyar Democrat su je su nemo masa burodi, inda ya dauka su 'yan kawo abinci ne.

Littafin ya yi bayanin cewa Mista Trump ya bayyana haka ne ga ma'aikatan Sanata Chuck Schumer da Nancy Pelosi.

Maggie Haberman ta kuma wassafa tarihin kalaman nuna kin jinin 'yan luwadi da ake zargin Mista Trump.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN