Bayan zargin Alkali ya kwada wa Lauya mari a harabar Kotu, Hukumar shari’a a jihar Kebbi ta dakatar da wani Alkalin Kotu bisa zargin aikata rashin da’a

Bayan zargin Alkali ya kwada wa Lauya mari a harabar Kotu, Hukumar shari’a a jihar Kebbi ta dakatar da wani Alkalin Kotu bisa zargin aikata rashin da’a


Babbar Kotun jihar Kebbi ta kafa kwamitin gudanarwa da zai binciki zarge-zargen rashin da’a da ake yi wa wasu Alkalai biyu. Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

Ana zargin daya daga cikinsu Mustapha Umar-Maccido da gudu daga bakin aiki yayin da wani Umar Salihu-Kokami aka ce ya mari wani Lauya da wasu mutane biyu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Magatakardar babban Kotun jihar Kebbi, Hussaini Abdullahi Zuru ya fitar a Birnin Kebbi ranar Juma’a.

Ya ce Umar-Maccido zai ci gaba da dakatarwa yayin da Salihu Kokami ya koma hedikwatarsa.

“An yi zargin cewa babban Alkalin Kotun Majistare Mustapha Umar-Maccido ya gudu daga bakin aikinsa na babbar Kotun Majistare, Kalgo, tun watan Satumbar 2022, bayan karewar hutun sa na makonni biyu.

“An zarge shi da yin aiki na sirri a wasu hukunce-hukuncen na Lauyoyi masu zaman kansu duk da cewa shi babban Alkali ne na gwamnati.

"Saboda haka, an dakatar da shi har sai lokacin da rahoton kwamitin gudanarwa da aka kafa don bincikar lamarin."

Abdullahi Zuru ya kara da cewa Salihu Kokani na babbar kotun Majistare ta III da ke Birnin Kebbi an dawo da shi hedikwatar ne saboda rashin da’a.

Ya ce: “Akwai zargin da babban Lauya kuma babban Sakatare na ma’aikatar shari’a ya yi masa na rashin da’a, cewa a ranar 12 ga watan Satumba, ya mari wani Lauyan jihar, Abdullahi Bawa Dan Bauchi da wasu mutane biyu.

“Wannan matakin ya faru ne a harabar babbar Kotun Majistare ta daya, a Birnin Kebbi, wadda aka ba shi alhakin karbar karar wasu ma’aikatan ma’aikatar ilimi mai zurfi.

“Saboda haka, ofishin babban Magatakardar na bayar da umurnin a dawo da shi zuwa hedkwatar, har sai an kammala rahoton kwamitin gudanarwa da aka kafa domin binciken lamarin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN