Yanzu yanzu: Wata karamar hukumar Najeriya ta hana yin acaba, duba dalili
Karamar hukumar Okitipupa ta jihar Ondo ta hana zirga-zirgar babura na kasuwanci a yankin daga karfe 6:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe.
Mista Akinrinwa Igbekele, shugaban karamar hukumar Okitipupa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Litinin a Okitipupa, cewa sun yanke shawarar tsaurara matakan tsaro a yankin.
Ya ce wani mataki ne na tunkarar kalubalen satar mutane da fashi da makami da sauran miyagun ayyuka a jihar.
Igbekele ya ce an tura tawagar sa ido domin kame tare da damke duk wani babur da ya saba wa doka.
“Mun shaida rashin tsaro a wasu yankunan jihar, duk da cewa a nan ba mu ga irin haka ba, amma hakan ba yana nufin mu nade hannayenmu muna kallo ba.
“Mun dakatar da Okada daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a matsayin wani mataki na dakile duk wani rashin tsaro da sauran munanan ayyuka a nan,” in ji Igbekele.
Sai dai ya ce Majalisar na hada kai da dukkan hukumomin tsaro domin daukar matakin gaggawa kan duk wani abu da ya shafi tsaro.