Yanzu yanzu: Gwamna Bagudu ya rusa Mmajalisar zartarwa ta jihar Kebbi

Gwamna Bagudu ya rusa Mmajalisar zartarwa ta jihar Kebbi


Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya amince da rusa Majalisar zartarwa ta jihar Kebbi daga ranar Laraba 7 ga Satumba, 2022. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin jihar, Babale Umar Yauri da aka rabawa manema labarai a wannan Laraba.

Maigirma Gwamnan yana godiya kwarai da irin gudumawar da kowane memba na Majalisar zartarwa ke bayarwa tare da gode musu bisa jajircewarsu wajen ganin sun tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar a tsawon lokacin da suke kan mukamansu. 

Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya kuma yabawa daukacin ‘yan Majalisar da aka rusa bisa yadda suka gudanar da ayyukansu yayin da nan ba da jimawa ba za a sanar da sabuwar Majalisar zartarwa ta jiha.

Sanarwar ta nuna cewa za a iya sake nada wasu daga cikin mambobin Majalisar da aka rusa da kuma wasu daga waje .

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN