Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama wani mutum mai suna Chisom Nweke ‘M’ mai shekaru 26 a garin Umuawulu, Awka a hanyar Amawbia, bisa zarginsa da damfarar ma’aikatan POS ta hanyar amfani da laya.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu ya fitar, ta ce wanda ake zargin ya amsa laifin yin amfani da laya wajen damfarar ma’aikatan POS a Awka da kewaye.
Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya yanke farar takarda mai girman kudi tare da baiwa ma’aikacin POS ya ajiye. Ana kokarin kama wasu 'yan kungiyar.