Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wata mata mai suna Ogochukwu Onuh, a unguwar Umuopu da ke garin Enugu Ezike a karamar hukumar Igbo-Eze a jihar Enugu. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Matar, wacce aka ce matar wani mutum mai suna Akada ce, wanda tsohon shugaban masu lura da unguwanni a cikin al’umma ne, an harbe ta ne a daren Juma’a, 9 ga Satumba, 2022.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai hari gidan Akada amma ya samu nasarar tserewa inda suka harbe matarsa.