Yan bindiga sun kai farmaki bankuna uku, sun tafka barna a jihar Arewa


Wasu da ake zaton 'yan fashi da makami ne ɗauke da bindigu sun farmaki rassan bankuna uku, UBA, Zenith da kuma First Bank a yankin Ankpa, jihar Kogi, inda suka kwashi kuɗi iya son ransu.

Yan Fashin, adadin mutum 20, an ce sun shiga garin da misalin ƙarfe 2:00 na rana. Da farko suka farmaki bankin UBA, daga nan suka zarce Bankin Zenith, daga bisani suka mamaye First Bank.

Daily Trust ta ruwaito wani da lamarin ya faru a idonsa na cewa maharan sun shiga garin kan ƙananan Motoci, Bas-Bas da Babura.

Shaidan ya bayyana cewa bayan fashi a Bankunan uku da masu POS mafi kusa, maharan sun kwashe kusan awa guda suna cin karen su babu babbaka. Yace yan bindigan sun fita garin suna harbi kan mai uwa da wabi.

Sun fita garin ta kan Titin Okpo, amma babu wanda ya iya leƙo wa daga cikin gida domin maharan sun buɗe wuta ba ƙaƙƙauta wa. Mafi yawan mazauna Ankpa har yanzun suna ɓoye basu fito ba," Inji shaidan.

Shin an rasa rayuka a harin?

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton babu tabbacin ko akwai wanda ya rasa rayuwarsa sanadiyyar harin.

"Ba zamu ce kai tsaye babu wanda harin ya taba ba, harin ya kwashe sama awa guda," Inji wani mai suna Ahmed, mazaunin garin Ankpa.

Wani mazaunin kuma ya faɗa mana cewa bayan yan bindigan sun gama aiwatar da nufinsu, rundunar haɗin guiwa ta jami'an tsaro suka nufi yankin da lamarin ya faru.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda reshen jihar Kogi, SP William Aya, bai ɗaga kiran waya ko amsa sakonnin da aka tura masa kan lamarin ba.

Gwaraazan jami'an yan sanda a jihar Katsina sun kubutar da ɗan takarar kujerar majalisar jiha karkashin inuwar PDP a Kankiya.

Mai magana da yawun yan sanda, SP Gambo Isah, ya tabbatar da nasarar bayan gumurzu da maharan da daren Asabar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN