Yadda wata uwargida kuma Lauya ta mutu yayin da take bin mijinta da tsananin gudu a cikin mota bayan ta kama shi da budurwa a kantin sayar da kayaki

Motar da Claret Opara ta yi hadari

An samu karin bayani kan Lauyan da ta mutu a wani hadari yayin da take bin mijinta da gudu a cikin mota a Calabar ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba. Shafin isyaku.com ya samo.

Marigayiyar mai suna Claret Opara da mijjnta Bassey Sunday sun yi aure sama da shekaru 10 da suka gabata, suna da ‘ya’ya uku.

A cewar jaridar The Nation, a ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba, ta samu kiran waya daga daya daga cikin kawayenta cewa an ga mijin nata a wani kantin sayar da kayayyaki tare da wata budurwa.

An ce ba tare da bata lokaci ba ta nufi katafaren kantin siyar da kayakin (Shopping mall).

Tana isa wurin, ta hangi mijinta yana shirin barin harabar kantin sayar da kayayyaki, a cikin motarsa ​​akwai budurwar wanda ake zargi mai suna Laticia.

Da ganin matar, ya yi sauri ya tafi tare da Laticia tana zaune a kujerar gaba.

Misis Bassey ta bi motar mijinta da tsananin gudun gaske, yayin da mijin ya yi ta kokarin tserewa wa matarsa sakamakon haka ya dinga zura gudun gaske da motarsa kuma matarsa ta biyo shi a cikin mota da gudu. Sai matar ta yi kokarin cim ma motar har suka isa babbar hanya.

Bassey Opara da matarsa Claret Opara

An ce mijin ya yanke shawarar kaucewa daga babbar hanyar zuwa titunan da ke makwabtaka da gidaje na jihar, lamarin da ya tilasta wa matar juyawar ba zata.

Daga nan motar ta kwace mata, sai ta rasa yadda za ta yi da motar, sannan ta kutsa cikin wata bishiya, lamarin da ya sa ta samu munanan raunuka, sannan motar ta yi mummunar barna.

Shaidun gani da ido sun ce nan take ya hango ta daga madubin baya cewa matar ta yi hatsari, sai mijin ya juyo.

Nan take budurwarsa ta sauka daga motarsa ta gudu daga wurin yayin da mijin ya yi gangami don ceto matarsa, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

An ce mijin ya yi ta kuka yana zubar da hawaye yana neman gafarar matarsa ​​da ke cikin jininta.

“Ya nemi afuwar matar, ya kuma roki kada ta mutu, sai ya garzaya da matar asibitin sojojin ruwa da ke Calabar inda aka tabbatar da mutuwar ta,” kamar yadda wani ganau ya shaida wa jaridar The Nation.

Abokan ma'auratan sun ce sun fara soyayya ne a lokacin da suke jami'a

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN