A wannan hoton, sojan Laberiya ne tsaye domin harbe daya daga cikin ministocin kasar mai suna Cecil Dennis bayan juyin mulki da sojoji suka yi a shekarar 1980.
A ranar 12 ga watan Afirilu ta shekarar 1980 ne Samuel Doe ya jagoranci juyin mulki wa shugaba William R. Tolbert a lokacin da shugaban kasar ke bacci, inda aka harbe shi, da kuma mutum 26 cikin magoya bayansa.
Bayan nasara akan juyin mulkin, sojojin Doe suka dauki ministocin kasar inda suka zagaya da su a cikin babban birnin Monrovia tsirara kafin daga bisani suka harbesu a bakin ruwa.
Da yawansu an kaisu kotu, amma alkalin kotun ya bawa masu karesu umarnin su takaita, daga bisani ya yanke cewar an samu ministocin da laifi, sannan ya yanke musu hukuncin kisa, wanda aka nuna kashesu a gidajen TV.
Bayan harbesu a bakin ruwa inda aka dauresu a jikin itace tareda basu umarnin su cire rigunansu, Cecil Dennis ne kawai bai mutu a harbin farko ba, daga baya sojoji suka kara bude masa wuta, wanda hakan ta sa aka yita harbin sauran ministocin har kusan harbi 60.
Minista daya daga cikin ministocin da ba a kashe ba itace Ellen Sirleaf, shugabar kasar da ta gabata. Itace ministar kudi. Tana ganin ba a kashe ta ba ne saboda mahaifiyarta ta taba bawa Samuel Doe din da sojojinsa ruwa suka sha.
Amma bayan shekaru 10 da faruwan wannan, shi ma Samuel Doe din ya gamu da nashi bala'in, bayan da aka azabtar da shi, aka tubeshi tsirara aka yi yawo da shi akan titin Monrovia. Aka yanke masa kunnuwa, aka cire masa yatsu, sannan kashe gari aka daddatsa jikinsa, aka dafa aka cinyeshi.
Credit: Farouq Farouk