Obasanjo ya ce ya tafka kuskure da ya goyi Bayan Buhari a 2015, ya bayar da hujja

Obasanjo ya ce ya tafka kuskure da ya goyi Bayan Buhari a 2015 


Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana nadamar na goyon bayan takarar shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari a 2015. Shafin isyaku.com ya samo.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wata mawallafin yanar gizo, Ifedayo Agoro wanda ta hadu da shi a cikin jirgi. Legit.ng ta ruwaito.

Agoro ta bayyana bayanan nasu daya bayan daya ta shafinta na Twitter, inda ta bayyana cewa ta hadu da tsohon shugaban kasar kwanan nan kuma ta zauna a gefensa a cikin jirgin.

Ta ruwaito Obasanjo yana cewa:

“Na yi kuskure da na goyon bayan Buhari, bai san komai ba game da tattalin arziki. Mun yi tunanin zai yaki cin hanci da rashawa da rashin tsaro, sannan ya dauki mutanen da suka san tattalin arziki da ababen more rayuwa. Babban kuskure.”

Tsohon shugaban kasar ya kuma zargi matasan Najeriya da cewa ba su da wata manufa daya ta yaki da tsarin tsoffin yan siyasa.

Ya kara da cewa har sai matasa a Najeriya sun nuna aniyar sauya tsarin siyasar kasar, lamarin ba zai canja ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN