Mazauna yanki sun lakada wa wani mutum duka har lahira saboda yi wa wata tsohuwa mai shekaru 61 fyade bayan ya fara yi wa wata akuya fyade


Mazauna yankin Mthhunzini da ke lardin KwaZulu-Natal na kasar Afirka ta Kudu sun lakada wa wani mutum duka har lahira tare da kona gawarsa bisa zargin yi wa wata mata mai shekaru 61 fyade. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Kafofin yada labaran kasar sun bayyana cewa, matar da kyar ta tsallake rijiya da baya a lokacin da ta yi fafatawa bayan wanda ake zargin ya shiga gidanta a ranar Litinin, 5 ga watan Satumba. 

Hayaniyar akuyarta ce ta tashe ta a waje bayan mutumin ya yi wa dabbar fyade kafin ya yi ma tsohuwar fyade.

An kama wanda ake zargin kuma aka yi masa duka har sai da numfashinsa na karshe. Jama'ar yankin sun yi amfani da duwatsu da bulo don kashe shi sannan suka bar shi.

A halin da ake ciki kuma, ‘yan kasar Afirka ta Kudu sun yaba wa al’ummar yankin bisa wannan mataki da suka dauka, inda suka ce tsarin shari’a na fifita masu aikata laifuka a kasar. 

Da take tsokaci game da lamarin, wata Ruth ta ce an kashe mahaifiyarta da ’yar uwarta a unguwa daya. 

"Ba zan taɓa mantawa da wannan wurin Mtunzini ba, an kashe mahaifiyata tun ina yar shekara 11, an gano gawarta bayan kwana 7. Ba da daɗewa ba an kashe kanwar mahaifiyata bayan ta koma gida daga aiki. An kashe ta. Kusan mintuna 15 daga zamanta. Alhamdu lillahi wannan baiwar Allah ta samu lafiya." ta rubuta. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN