Khul'i shi ne mace ta fanshi kanta daga wajan mijinta ta hanyar ba shi sadakin da ya ba ta lokacin auranta kamar yadda matar Thabit Bn Kais bn Shammas ta yiwa mijinta a hadisin da ya tabbata a manyan Kundayan Musulunci. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa, ya ce ya halatta a shariar Allah mace ta yiwa miijnta Kul'i in har ta ga ba za ta iya tsayawa da hakkokinsa na aure ba, kamar yadda aya ta (229)a suratul BAKARA ta tabbatar da hakan.
À zance mafi inganci Kuhl'i yana saukar da saki daya, sai dai yana nisanta mace da mijinta ta yadda ba zai iya saké zama da matar ba, sai in ya bayar da SADAKI sannan an kara daura sabon aure.