Gwamnan arewa ya buga kirji, ya ambato dalilin samun kwarin guiwar nasarar Tinubu a 2023
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara a ranar Asabar ya ce jihar za ta ba Bola Ahmed Tinubu kuri’u masu tarin yawa domin ya zama shugaban kasa a Najeriya a 2023.
AbdulRasaq ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin da yake kaddamar da ofishin yakin neman zaben shugaban kasa mai zaman kansa na kungiyar Arewa ta Tsakiya na Asiwaju (NCAA) da kuma Kudu maso Yamma Asiwaju (SWAGA), a Fate Road Ilorin.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Raji Rasaq, ya ce ayyukan da ya yi a ofis, tare da yin tasiri a fadin jihar, ya tabbatar da cewa Hwamnatin APC ta fi dacewa kuma za ta iya tallata Asiwaju da sauran ’yan takarar jam’iyyar. jam'iyya.
Ya ce duka NCAA da SWAGA, da sauran kungiyoyin tallafi, wadanda ke da kwarin gwuiwa don tabbatar da aniyar Asiwaju.
Ya ce jihar Kwara na daya daga cikin jihohin da suka bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri’u masu rinjaye a zaben 2019, yana mai cewa har yanzu jama’a sun kuduri aniyar yin irinsa ga Tinubu ya zo 2023.
Ya kuma yi kira ga mabiya jam’iyyar a jihar da su jajirce, su mai da hankali ba tare da sunkuyar da kai ba, inda ya bukaci su yi aiki tukuru domin samun nasarar jam’iyyar a fadin kasar nan.