Girma zai fadi: Kotu ta umarci Kwamishinan Yan sanda ya kamo wasu Sarakuna biyu ya durkusar da su a gabanta, duba dalili


Kotun Majistare da ke Akure, babban birnin jihar Ondo, a ranar Juma’a, 9 ga watan Satumba, ta bayar da sammacin kamo wasu mutane biyu da suka bayyana a matsayin Sarakunan gargajiya a Irele da Igodan Lisa a kudancin jihar. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Bayan shigar da karar Charles Titiloye, babban lauya kuma Kwamishinan shari’a na jihar Ondo, Kotun ta umurci kwamishinan ‘yan sandan da ya gabatar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

A makon da ya gabata ne Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ya bayar da umarnin kama wadanda ake zargin tare da gurfanar da su gaban kuliya.

An zargi Ademola Idowu Oloworiyibi da hada baki da wasu wadanda har yanzu ba su kai ga karbar sarautar Olofun na Irele ba bisa ka’ida ba, wanda aka ce ya sabawa kuma hukuncin da ya dace a karkashin sashe na 516 na kundin laifuffuka na jihar Ondo, mai lamba MAK. /423C/2022 wanda babban mai shari'a ya shigar da shi a gaban babban kotun Majistare dake Oke Eda, Akure.

Har ila yau, an tuhumi Oloworiyibi da laifin yin aiki ba tare da amincewar majalisar zartarwa ta jihar Ondo ba, kuma ya saba wa sashi na 15 (1) da (2) na dokar sarakunan jihar Ondo ta hanyar ba da damar nada shi tare da bayyana kansa a matsayin Olofun na Irele.

Hakazalika, an tuhumi Adeyemi Akinde da laifin hada baki tare da dora shi ba bisa ka’ida ba a matsayin Olu na Igodan Lisa wanda ya sabawa dokar sarakunan jihar Ondo a tuhume-tuhume na biyu mai lamba MAK/424C/2022.

A halin da ake ciki dai an dakatar da shari’ar mutanen biyu bayan sun kasa gurfana a gaban kotun

Alkalin kotun, FA Aduroja ya umurci Kwamishinan ‘yan sandan da ya kama su tare da gabatar da su a ranar da za a ci gaba da sauraron karar.

Daga nan an dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga Satumba, 2022.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN