Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta tabbatar da yin garkuwa da mataimakin shugaban karamar hukumar Isoko ta Arewa a jihar Delta, Frank Esiwo Ozue. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Esiwo a ranar Lahadi 12 ga watan Satumba, a garin Ogor da ke karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Patani.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta, Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin sannan kuma ya bayyana cewa suna kokarin ceto mataimakin shugaban LG.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa ‘yan bindigar sun bar mota da wayoyin mataimakin shugaban kuma har yanzu ba su tuntubi ‘yan uwa domin neman kudin fansa ko kuma inda yake ba.