BAYAN MAYAR DA RARAR NAIRA DUBU 50 GA ALAZAI, HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAN BAUCHI ZATA FARA AIKIN UMRAH

BAYAN MAYAR DA RARAR NAIRA DUBU 50 GA ALAZAI, HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAN  BAUCHI ZATA FARA AIKIN UMRAH

Daga Muazu Hardawa, a Bauchi


Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Bauchi ta shirya domin fara gudanar da aikin Umrah a wannan shekarar ga dukkan Musulman da ke bukata. 

Bayan haka Alhazan da suka biya kudi basu samu tafiya ba suma suna iya biya daga cikin kudin da suka biya na ajiya domin zuwa aikin Umrah, daga baya idan suna bukatar zuwa aikin Hajji sai su cikata kafin a tafi aikin Hajji na shekara mai zuwa wato 2023.

Sakataren hukumar Dokta Abdurrahman Ibrahim Idris shine ya bayyana haka cikin hirarsa da Manema  labarai a ofishin sa, inda yace Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na Jihar Bauchi ya sahale wa hukumar ta fara gudanar da aikin Umrah a bana.

Don haka ya ce a yanzu sun kammala shirin bitar aikin Hajjin da ya gudana nan ba da jimawa ba za su fara shirin na shekara mai zuwa da zarar sun samu umarni daga hukumar aikin Hajj ta kasa NAHCON za su bude ci gaba da karbar kudin maniyyatan shekara mai zuwa.

Sheikh Abdurrahman Ibrahim Idris ya kara da cewa hukumar aikin Hajj ta kasa ta dawo da naira dubu Hamsin ga kowane Alhaji da ya tafi aikin Hajji da ya gabata na 2022,  kuma tuni sun bi Alhazan zuwa kananan hukumomin su an basu kudaden su.

Bayan haka hukumar ta rabawa sama da Alhazan 1400 rarar wannan kudi da kuma ruwan zamzam Lita biyar kyauta ga kowane Alhaji. Haka kuma duk wanda ya biya a shekarar da ta wuce bai samu tafiya ba idan yana bukatar a maida masa kudin sa don ya juya ko ya yi wata bukata sai ya kawo shaidar biyan kudin kuma nan take za a tura masa kudin zuwa asusun ajiyarsa.

Ya kara da cewa har mutanen da Gwamnati ta biya musu duk mai bukatar kudin za a maida masa, idan kuma.yana so zai iya barin kudin don fara shirin tafiya a shekara mai zuwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN