Bayan kama wata mata ta yi tatil da barasa yayin da take tukin mota, duba abin da ta yi a cikin Kotu


Wata kotun kula da zirga-zirgar ababen hawa a birnin Nairobi ta tsare wata mata da ta yi shaye-shaye kuma ta buge da barci a lokacin da ake shari'a. 

An gurfanar da Sharon Oparanya a gaban mai shari’a Martha Nanzushi a safiyar ranar Alhamis, 22 ga watan Satumba, domin amsa laifin tuki cikin maye. 

Sai dai kuma ta kwanta a kan benci ta fara barci daga bisani ta fara hansari da karfi.

"Dakata! Me ya sa take huci a kotu, wani ne ke kwana a kotuna?" Alkali ya fada.

A martanin da jami'in  kotu ya bayar, ya ce Oparanya ta bugu da barasa ne, shi ya sa take barci a kotu.

Biyo bayan dagula lamarin, alkalin kotun ya umarci a tsare Oparanya a gidan yarin mata na Lang'ata har zuwa ranar Juma'a inda za ta amsa tuhumar da ake mata.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN