Bala'i ya far wa Turji, ya sha da kyar ya gudu daga mabuyarsa bayan mayakansa 12 da yan uwansa sun mutu sakamakon luguden bamabaman jiragen yakin Najeriya a maboyarsa ta jihar Zamfara
Kimanin sa’o’i 24 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da jami’an tsaro a ranar Alhamis din da ta gabata an kashe ‘yan bindiga da dama yayin da dan ta’addan, Bello Turji, ya tsere da kyar. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban kasar, a yayin taron kwamitin tsaro na kasa a Abuja, a cikin mako, ya yabawa hukumomin tsaro kan nasarorin da aka samu a baya-bayan nan wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane a kasar.
Shugaban wanda ya jagoranci taron, ya bukaci hukumomin tsaro da su hada karfi da karfe kan nasarorin da aka samu a kafin watan Disamba.
A baya dai Buhari ya bayar da umarnin yin tattaki ga jami’an tsaro da su bi su kakkabe duk wani nau’in ta’addanci a kasar nan musamman ‘yan fashi da garkuwa da mutane.
NAN ta samu labarin cewa akalla mayaka 12 da ‘yan uwan fitaccen sarkin ta’addanci, Turji, sun mutu a wani samame da sojojin saman Najeriya suka kai maboyar Turji a unguwar Fakai a yankin Shinkafi, da yammacin ranar Asabar.
‘Yan ta’addan da lamarin ya shafa, wadanda ake kyautata zaton suna halartar bikin nadin wani yaro a gidan Turji, sun gamu da ajalinsu sakamakon harin bam da aka kai masu.
NAN ta ruwaito cewa an kashe wasu ‘yan ta’adda da dama a karshen makon da ya gabata sakamakon fadan da aka yi tsakanin wasu kungiyoyin ta’addanci a shiyyar Arewa maso Gabashin kasar nan.