Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a ranar 1 ga watan Satumba ta kama wani matashi dan shekara 45 bisa laifin lalata karamar yaro dan shekara 10 a garin Tsohon Tike da ke karamar hukumar Mayo Belwa. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Wanda ake zargin mai suna Kawu Sale, mazaunin karamar hukumar Tsohon Tike Mayo Belwa, kuma makwabcin mahaifin yaron, an yi zargin ya shigar da yaron zuwa cikin dakinsa da karfin tsiya ya yi lalata da shi ta duburarsa.
Mahaifin wanda abin yaron, Akure Usman tare da sauran jama’ar yankin ne suka kai rahoton faruwar lamarin ga hedikwatar ‘yan sanda da ke Mayo Belwa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya ce binciken farko da aka gudanar ya zuwa yanzu ya nuna cewa a daidai wannan rana da misalin karfe 1100 na safe ne aka hangi wanda abin ya shafa a guje daga dakin wanda ake zargin. Da aka yi masa tambayoyi, yaron bayyana abin da wanda ake zargin ya yi masa.
''A fusata da abin da wanda ake tuhuma ya yi, sai makwabta suka nufi dakin wanda ake zargin. Amma da ya ga gungun mutanen sun nufo dakinsa, sai ya yi yunkurin kashe kansa ta hanyar daba wa kansa wuka da dama a wuya da cikinsa.” Inji Nguroje.
Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP SK Akande, ya umurci jami’an hukumar CID na jihar da su dauki nauyin bincike tare da tabbatar da gurfanar da shi a gaban kotu.
A halin yanzu dai wanda ake zargin yana kwance a asibiti yana karbar magani a wani asibiti da ke Yola.