Wasu ’yan bindiga a ranar Litinin, 1 ga watan Agusta, sun kai hari kan Hajiya Ageji Omale wacce ta kasance tsohuwar shugabar mata ta jam’iyyar APC mai mulki a karamar hukumar Omala ta jihar Kogi. Kafar labarai na Isyaku News Online (Isyaku.com) ya samo. Jaridar legit.ng ta wallafa.
PM News ta ruwaito cewa Omale na cikin barci ne lokacin da maharan suka kai farmaki gidanta da ke karamar hukumar Abejukolo-Ife a jihar, inda suka harbe ta sannan suka bace.
Bayan an bar ta a cikin jininta, kukan da tsohuwa ta yi na neman agaji ya jawo hankalin makwabta inda suka garzaya da ita ofishin ‘yan sanda domin gabatar da rahoto kafin a kai ta babban asibitin Abejukolo.
Wani mazaunin unguwar da ya san Omale ya ce:
“Dukkanmu muna cikin gida tare da mazauna nesa da gida a gonakinsu, sai muka ji karar harbe-harbe, daga baya kuma muryar Mama tana ihu mai zafi. Maharan ta sun gudu kafin isowar mu.
“Mun yi mamaki domin Hajiya mutum ce mai son zaman lafiya kuma uwa ce ga kowa da kowa. Muna addu'ar 'yan sanda sun fatattaki masu laifin da masu daukar nauyinsu domin hakan yana nufin ba mu da tsaro a gidanmu."
Nigerian Tribune, a rahotonta, ta ce kokarin jin ta bakin jami’in ‘yan sandan Omala (DPO) ta wayar salula ya ci tura ya zuwa yanzu.