Karshen lamari: Kotu ta yankewa kasurgumin dan bindiga hukuncin zaman gidan magarkama


Babbar kotun Abuja karkashin mai shari'a Binta Kyako ta yankewa kasugumin dan bindigan da ya addabi wani yankunan jihar Taraba.

Bayan shafe lokaci ana shari'a, an kama Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume da laifukan da ake tuhumarsa, kana aka daure shi zaman shekaru bakwai a gidan yari.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, Wadume zai yi zaman magarkama ne tare da wasu mutane biyu da ake tuhumarsu tare.

Rahoton Daily Trust ya ce, an yanke hukuncin ne a ranar 22 ga watan Yuli, amma aka sanar da manema labarai a yau Litinin 15 ga watan Agusta.

A baya an gabatar da tuhume-tuhume 13 kan Wadume, inda Nyako ta same shi da laifuka biyu.

Hakazalika, wani sufeton dan sanda zai yi zaman shekaru uku a gidan yari bisa laifin boye laifi da aka gabatar a gaban kotun.

Jami'an mai suna Ali Dadje, an ce yana aiki ne a ofishin 'yan sanda da ke karamar hukumar Ibi a jihar Tarana.

Baya ga daure dan ta'adda Wadume da Dadje, sauran tsagerun da aka daure su sun hada da Auwalu Bala (Omo Reza), Uba Bala (Uba Delu), Bashir Waziri (Baba Runs), Zubairu Abdullahi (Basho) da Rayyanu Abdul.

Sai dai, Nyako ta wanke tare sallamar Omo Razor da Baba Runs saboda shaidun da suka bayyana.

A bangare guda, Delu, Abdullahi da Abdul za su yi zaman shekaru bakwai a gidan kasa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN