Jihar Kebbi: 'Dan Bagudu' ya magantu kan wani lamari da ya shafi koyar da harkar noman zamani da zai kawo kudi ga matasaGwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya ce noma na kan gaba wajen hada-hadar kudi ga Najeriya kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shi fifiko. Shafin Isyaku News Online isyaku.com ya samo.

Bagudu ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin a Birnin Kebbi a wajen bude taron koyawa matasa sana’o’in hannu da karfafa gwiwar matasa na tsawon kwanaki biyar.

Hukumar kula da kayayyakin more rayuwa ta kimiyya da injiniya ta kasa (NASENI) ce ta shirya shi, mai taken: “Hanyoyin noma na zamani ta hanyar amfani da ingantaccen aikin noma a jihar Kebbi”

Gwamnan ya ce Buhari ya jajirce sosai wajen kawo sauyi a harkar noma ta hanyar samar da isassun kudade na Kimiyya da Injiniya, yana mai cewa, “noma ilimi ne.

A cewar Bagudu, kimiyya na kara habaka amfanin gona a fadin Najeriya tare da rage matsalolin da suka shafi fannin.

Shugaban kungiyar Gwamnonin APC ya ci gaba da cewa, kimiya na inganta kayan amfanin gona da abin da ake samu kuma Buhari ya nuna himma wajen ganin Najeriya ta dogara da kanta wajen samar da abinci.

Ya ce akwai damammaki ga matasa a harkar noma, yana mai cewa, "zaku iya zama hamshakan masu kudi kuma ku kasance daidai da takwarorinku a fadin duniya."

Tun da farko, mataimakin shugaban hukumar NASENI, Farfesa Muhammed Sani Haruna ya ce an shirya taron horon na kwanaki biyar domin wayar da kan mahalartan dabarun noman zamani da injina.

Ya ce tilas ne Najeriya ta kawar da tsarin noma na gargajiya, sannan ta yi amfani da fasahar zamani don kawo sauyi kan yadda ake nomawa don samar da abinci, wadata da kuma fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN