Sabon Kwamishinan Yan sandan jihar Kebbi CP Magaji Ahmed Kontagora, ya karbi mulki daga CP. Musa Baba, psc(+) wanda ya yi ritaya daga aikin 'yan sandan Najeriya. Shafin labarai na Isyaku News Online isyaku.com ya samo
Kakakin hukumar Yan sandan jihar Kebbi SP Nafi'u Abubakar ne ya sanar da haka a wata takarda da ya aike wa manema labarai a Birnin kebbi.
Nafi'u ya ruwaito cewa CP Magaji Ahmed Kontagora ya fito ne daga karamar hukumar Kontagora ta jihar Neja kuma ya shiga aikin ‘yan sandan Najeriya a ranar 3 ga Maris, 1990, a matsayin mataimakin Supritendan ‘yan sanda.
Ya yi aiki a matakai daban-daban a cikin umarni da tsari daban-daban na hukumar yan sandan Najeriya.