Ta faru: An kama wani saurayi infoma dan leken asiri da ke yin shigar mata yana ba yan bindiga bayanan sirri (Hotuna)


An kama wani da ake zargin mai yiwa ‘yan fashi da yan bindiga leken asiri ne bayan ya yi shigar mata a jihar Katsina. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

A cewar wani Umar Abduladi Jibia, an kama wanda ake zargin ne a ofishin hukumar sufuri ta jihar Katsina (KSTA) da ke karamar hukumar Jibia a ranar Juma’a, 26 ga watan Agusta. 

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da wasu ‘yan bindiga suka tare hanyar Katsina zuwa Jibia tare da yin garkuwa da wasu fasinjoji da ba a tantance adadinsu ba, inda suka kashe daya.Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN