Ba ainihin hoton Labarin bane |
Ya ce wa Salele ya je ya yi tunani a kan tayin ya kuma tantance hukuncin da ya yanke a ranar 6 ga watan Satumba, ranar da aka dage ci gaba da shari’ar sa.
Mahaifiyar Bilikisu, Rayila Lawal, ta maka Salele a gaban kotu inda ta bukaci ta tilasta masa ya auri diyarta idan yana sonta da gaske ko kuma ya bar ta idan bai shirya yin aure ba.
“Muna zaune a wuri daya kuma yana zuwa ya gana da ‘yata ba tare da yardar mu a matsayin iyayenta ba.
“Na sadu da mahaifiyarsa don sanar da ita batun kuma ta ce danta bai shirya yin aure ba.
“Salele ya canza dabara kuma ya daina ziyartar ’yata amma ya ci gaba da kiran ta a waya don saduwa da shi a wuraren da ya shirya.
“Ba na son ya bata tarbiyyar da na yi wa ‘yata tsawon shekaru, shi ya sa na yanke shawarar kai shi kotu,” in ji Rayla.
Ta nanata cewa a shirye ta ke ta aurar da ‘yarta idan har Salele ya shirya.
A nasa bangaren, Salele ya ce yana son yarinyar amma bai yi shirin aure ba sai bayan shekara biyu.
“Ni dalibi ne da nake karatu a daya daga cikin jami’o’in tarayya kuma ba zan so aure ya dauke ni ba.
“Bayan haka, ba ni da sadaki kuma har yanzu ina zaune da iyayena,” Salele ya shaida wa kotu.