Wata babban Kotun jihar Kebbi da ke zamanta a garin Birnin kebbi ranar Laraba 6 ga watan Yuli ta yanke wa Suleiman Idris hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta kama shi da laifin kashe Sadiya Idris da diyarta. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.
Mai shari'a Jastis Muhammad Sulaiman Amburrsa ya kama Sulaiman da laifin kisa ne bayan ya ki amincewa da uzurin da Lauyan Sulaiman ya kawo cewa mariganya Sadiya ta harzuka Sulaiman ne watau "Provocation".
Lauyan ya ce Sadiya ta gaya wa Sulaiman kalamai da suka bata masa rai, cewa "Jahili wulakantaccen maigadi..." da dai sauransu.
Sai dai Kotu ka ki amincewa da uzurin bisa hujjar cewa Sadiya ta gaya masa kalaman ne da misalin karfe 10 na safe, amma sai karfe 2 na dare ya je ya kashe ta. Kotu ta ce abin da Sulaiman ya aikata ya zarce abin da Sadiya ta yi masa, kari da cewa diyarta bata yi masa laifi ba amma duk ya kashe su.
Sakamakon haka Alkalin Kotun Muhammad Sulaiman Ambursa ya kama Sulaiman Idris da laifin kisan Sadiya da diyarta kuma Kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya har sai ya mutu.