Yanzu muke samun labarin cewa, ALlah ya yiwa fitaccen daraktan masana'antar Kannywood, Nura Mustapha Waye.
A rahoton da muka samu daga kafar labarai ta DW ya ce, wasu makusanta sun ce an rabu da marigayin da daren jiya cikin koshin lafiya.
Mustapha dai shi ne daraktan wannan shirin mai dogon zango da ya shahara a duniyar Hausawa, wato Izzar So.
Babban jarumin gaba-gaba a shirin fim din na Izzar So a shafinsa na Instagram ya sanar da rasuwar daraktan a wani rubutu da ya yi.
A cewarsa:
"Innalillahi wainnailaihirrajiun Allah Ya Karbi Rayuwar Nura Mustapha Waye Director IZZAR SO Za Ayi Zanaidarshi Karfe 11 Na Safennan A Gidansa Goren Dutse Primary Insha Allah, Allah Ya Yafe Masa Kurakuransa Amin, Allah Yasa Idan Tamu Tazo Mu Cika Da Imani Amin."
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI