Mai martaba Sarkin Daura, Jihar Katsina, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya auri wata budurwa ‘yar shekara 22 mai suna A’isha Yahuza Gona. Shafin isyaku.com ya samo.
Kamar yadda majiyar ta zanta da Daily trust, an daura auren ne a garin Safana na jihar Katsina.
Majiyar ta kuma bayyana cewa, Sarkin ya auri A’isha ne a wata ‘yar karamar biki na gargajiya bayan ‘yar gajeriyar zawarcin da ta shafe sati guda ana yi.
Amaryar diyar tsohon shugaban karamar hukumar Safana, Alhaji Yahuza Gona ce.
Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa sabuwar Amaryar ta riga ta kasance a gidan aurenta da ke Daura.
Ku tuna cewa Sarkin ya auri wata mata ‘yar shekara 20, Aisha Iro Maikano, a watan Disamba, 2021.
A shekarar 2015 ne Sarkin ya auri wata budurwa mai suna Gimbiya Aisha Umar Farouk, kuma dukkansu sun haifi ‘ ya’ya biyu tare.