Hajj 2022: Mahajjatan Nijeriya sun taru a Dutsen Arafat da na sauran Duniya domin neman yardar Allah da yin addu'a


Alhazan Najeriya a kasar Saudiyya sun bi sahun miliyoyin alhazai na Duniya a Dutsen Arafa a wani bangare na aikin Hajjin shekarar 2022.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, haduwar Dutsen Arafat wani muhimmin bangare ne na aikin Hajji wanda ke baiwa mutane damar yin addu’a ga iyalansu da abokan arziki da kuma masoyansu don neman yarda da rahamar Allah.

Daya daga cikin ma'anar dutsen mai alfarma shi ne cewa a rana ta tara ga mahajjata sun tashi daga Mina zuwa dutsen Arafat inda suke tsayuwar tudu da addu'a da karatun kur'ani.

An fi kiran dutsen da Jabal ar-Rahmah, ma'ana dutsen rahama. An tattaro cewa manzon Allah mai tsira da amincin Allah a cikin kur’ani ya yi hudubarsa ta karshe a Duniya a dutsen mai cike da tarihi.

Muhimmancin Hajji Ga Musulmi

A Musulunci, aikin Hajji ya zo ne da tsarin da kowane mahajjaci zai yi la'asar a Dutsen Arafat kuma duk wani abu da ya saba wa haka, aikin Hajji ya baci.

Tsawon shekarun da suka gabata, an bayyana aikin Hajji a matsayin daya daga cikin manyan tarurrukan addini a Duniya domin ana sa ran kowane musulmi ya gudanar da aikin a kalla sau daya a rayuwarsa.

A aikin Hajjin shekarar 2022, sama da mahajjatan Najeriya 40,000 ne a jihohi daban-daban suka je kasar Saudiyya domin yin aikin Hajji.

Gumi, addu'a, soyayya: matsanancin zafi ya mamaye hajji

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa yanayin da ake ciki a kasar Saudiyya bai yi wa maniyyata dadi ba.

An tattaro cewa zafin Rana ya tashi zuwa kusan digiri 42 ma'aunin celcius (digiri 108 Fahrenheit).

Saboda yanayi an ga maza da dama na kokarin kare kawunansu daga zafin rana kuma Musulunci ya hana maza sanya hula a lokacin aikin Hajji.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN