Bayan korar AGF: Sunaye 20 na kan layi da ke neman maye gurbin Ahmed Idris


Kimanin Daraktoci 20 ne ke kan gaba wajen maye gurbin tsohon Akanta-Janar na Tarayyar Najeriya Ahmed Idris da aka kora kwanan nan kan badakalar Naira biliyan 80
.

Kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito, ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ya fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da cewa matakai sun fara nemo sabuwar AGF.

Legit.ng ta tattaro cewa Daraktocin da suka kai mataki na 17 a ma’aikatan gwamnati a ranar 1 ga watan Junairu 2020 ne kawai za a tantance su a matsayin Daraktoci.

An kuma yi imanin cewa babban sakatare a ma'aikatar kudi ya gabatar da jerin sunayen da dama domin tantancewa.

Mai kula da AGF, Anamekwe ya maye gurbinsa

Sai dai yayin da ake ci gaba da farautar sabon AGF, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Mista Sylva Okolieaboh, Darakta a sashen Treasury Single Account (TSA) ya maye gurbin Chukwuyere Anamekwe a matsayin mukaddashin Akanta Janar na Tarayya (AGF).

Kamar yadda jaridar ta ruwaito, an nada Anamekwe ne a matsayin mai rikon kwarya bayan sauke Ahmed Idris daga mukamin.

Rahotanni sun bayyana cewa, Anamekwe wanda aka nada a matsayin mai rikon kwarya shi ma yana fuskantar binciken hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, dalilin da ya sa ake ganin shi ma ya sanar da wanda zai maye gurbinsa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN