Sokoto: Tambuwal ya mayar da shugaban ma’aikata, ya nada kwamishinoni 9, duba sunaye


Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, ya mayar da tsohon shugaban ma'aikatan fadarsa, Alhaji Mukhtar Magori, tare da gabatar da kwamishinoni 9 a Majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya tattaro.

Wannan ci gaban ya biyo bayan samar da gibi a guraben aiki ne bayan da Yan Majalisar zartarwar jihar  suka yi a ranar 27 ga watan Afrilu don neman mukaman siyasa a jihar.

A wata sanarwa da Muhammad Bello, mai baiwa Gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar ta bayyana cewa an sake nada shida daga cikin kwamishinonin da aka nada domin cike gurbin.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa wasu daga cikin kwamishinonin da aka sake nada su ne wadanda bisa radin kansu suka fice daga takarar Sanata na jam'iyyar PDP a mazabunsu daban-daban.

Wasu kuma su ne wadanda suka maye gurbin kwamishinonin da suka ci tikitin tsayawa takarar kujerar Sanata.

Bello ya ce Kwamishinonin da aka sake nadawa sun hada da:  Aminu Bodinga, Rtd. Col. Garba Moyi, Bashir Gidado, Salihu Maidaji, Abdullahi Maigwandu and Abubakar Maikudi.

“Haka kuma an zabi Abdullahi Hausawa, Jami’in Hulda da Jama’a na PDP (PRO), Abubakar Dange da Bashir Lambara, a matsayin sabbin wadanda aka nada, domin cike guraben da ake da su,” inji shi. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN