Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo ya shawarci jam’iyyar APC da ta ci gaba da rike madafun iko ta hanyar mika ragamar shugabancin kasar zuwa yankin kudu a daidai lokacin da ta ke shirin gudanar da babban taro na musamman na zaben fidda gwani na shugaban kasa.
A ranar Larabar da ta gabata ne aka bayyana Akeredolu wanda ya zama shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Yamma a matsayin shugaban tsaro da bin doka da oda na babban taron jam’iyyar.
A wani takaitaccen sako da ya fitar ta shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, Gwamnan ya sake bayyana matsayin abokan aikinsa a kungiyar gwamnonin Kudancin Najeriya na cewa a mayar da mulki zuwa Kudu.
Akeredolu ya bayyana cewa dole ne jam’iyyar APC ta kasance a shirye ta rika karba-karba ta yadda za ta ci gaba da rike shugabancin kasar, inda ya kara da cewa don ci gaba da mulki; dole ne jam’iyyar ta juya shugabancin kasar zuwa Kudu.
“Dole APC ta yi aiki don ci gaba da rike madafun iko. Dole ne mu juya mulki don riÆ™e iko !!! Juyawa zuwa Kudu. Shikenan." Sakon ya ce.