Wani ganau ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa mutum na uku na kungiyar ya tsere.
Ya ce wadanda ake zargin sun sace babur ne a yankin ranar Talata bayan sun kwace babur daga hannun mutumin.
Ya kara da cewa an fatattake su har inda aka kama su, suka sha dan karen duka kuma aka kona su bayan sun gudu daga inda suka kwace babur din.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, DSP Adewale Osifeso, ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin
Rubuta ra ayin ka