Akalla mutane 22 sun yi mutuwar gaggawa a wani gidan rawa a Afirka ta Kudu, duba dalili


An kira agajin gaggawa da sanyin safiyar Lahadi 26 ga watan Yuni, zuwa Tavern Enyobeni da ke Scenery Park, a gefen gabashin London, lardin Gabashin Cape, a cewar shafin yada labarai na Daily Dispatch. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

Kakakin ‘yan sanda, Birgediya Tembinkosi Kinana ya shaida wa tashar talabijin ta Newzroom Africa cewa; 

"Mun samu rahoto game da [mutane 17] da suka mutu a wani gidan abinci a Scenery Park wanda ke gabashin London.

“Ana binciken al’amuran da suka faru a yayin da muke magana.

"Ba ma son yin wani hasashe a wannan matakin."

Kinana ya kuma bayyana cewa wadanda abin ya shafa na da shekaru tsakanin 18 zuwa 20. Jami’in sashin kula da harkokin tsaro na lardin Gabashin Cape, Unathi Binqose, da yake magana daga wurin, ya ce an samu turmutsutsu a matsayin musabbabin mutuwar.

Jaridar cikin gida, DispatchLive, ta ruwaito “gawawwakin suna kwance a kan tebura, kujeru da kuma Æ™asa; ba tare da bayyana alamun rauni ba”.

Hotunan da ba a tantance ba da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna gawarwakin da ba a ga alamun raunuka ba, sun baje a filin kulob din.

Gidan talabijin na cikin gida ya nuna jami'an 'yan sanda suna kokarin kwantar da hankulan gungun iyaye da 'yan kallo da suka taru a wajen kulob din a birnin, wanda ke gabar tekun Indiya, kusan mil 620 (1,000) kudu da Johannesburg.

Siyanda Manana, mai magana da yawun sashen kiwon lafiya na lardin Gabashin Cape, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters:

" Nan take za mu fara gudanar da binciken gawarwakin mutane domin mu san dalilin da zai iya haddasa mutuwar, muna magana ne a kan gawarwaki 22 a yanzu."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN