Ahmed Yerima ya bayyana dalilin da ya sa ya bullo da tsarin shari’a a jihar Zamfara


Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Yerima ya bayyana dalilin da ya sa ya bullo da tsarin shari’a a jihar. 

Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a 6 ga watan Mayu, tsohon gwamnan ya ce ya gabatar da tsarin shari’a a jihar kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada kan ‘yancin addini.

Da yake tsokaci game da yadda ake kallonsa a matsayin mai tsattsauran ra'ayin addini, Yerima ya bayyana hakan a matsayin "jahilci", ya kara da cewa yana daya daga cikin abubuwan da zai yi yaki idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya. 

Yace; 

“A kan batun Shari’a, ni Musulmi ne kuma duk inda na je ina cewa ni Musulmi ne, kuma ina son in mutu a matsayina na Musulmi. Kamar yadda na ce, zan yi yaki da matsalar jahilci kuma wannan yana daya daga cikinsu.

“Mutane ba su sani ba; da yawan mutane ba su san cewa kundin tsarin mulkin Najeriya sashe na 38 ya tanadi ‘yancin yin addini ba, ciki har da ‘yancin canza addininka idan kana so, ka yi shi kadai, ko kuma a cikin jama’a, a boye ko a cikin jama’a.

“Don haka a matsayina na gwamnan jihar na bi dokar da kundin tsarin mulki ya tanada, na shirya doka, na aika da ita majalisar dokokin jihar suka amince da ita kuma na aiwatar da abin da tsarin mulkin Najeriya ya ba ni ikon yi a jihar Zamfara.

“Ban taba bukatar ko tambaya ko tilasta wani Kirista ya bi addinin Musulunci ba, domin da na yi wani abu da ya sabawa tsarin mulkin kasar nan.

“Don haka idan aka zabe ni da yardar Allah za a zabe ni a karkashin tsarin mulki kuma zan yi rantsuwar kare kundin tsarin mulkin Najeriya. Ba zan taba yin wani abu da ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa ba.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN