Ta faru: Malaman jami'a sun dauki mataki bayan Buhari ya dakatar da albashinsu


Ma’aikatan da ke yajin aikin a jami’o’in Najeriya, a ranar Talata sun bayyana manufar ba za su yi aiki ba matukar ba a basu albashi ba inda suka ce yajin aikin gargadi yanzu ya koma na sai baba-ta-gani
.

Ma’aikatan a karkashin kungiyar malaman fasaha ta kasa (NAAT), sun ce dakunan gwaje-gwaje, wuraren bita, gonaki da sauran su za su kasance a rufe har sai gwamnati ta biya su albashi.

Daily Trust ta ruwaito cewa ma’aikatan sun bayyana raddi ne ga sanarwar da gwamnatin tarayya ta yi na cewa ba za a biya su albashi ba a lokacin yajin.

Da yake magana a madadinsu a Abuja, Shugaban NAAT, Ibeji Nwokoma, ya bukaci mambobinsa da su doge, kuma kada su bari dabarar “rarraba kai da mulki” na gwamnati ya rage musu kwarin gwiwa.

Ya bayyana cewa:

“A yau an ware kungiyarmu da ASUU domin aiwatar da manufar “Babu aiki, Babu albashi”.

“Ya ku abokai, ni, shugaban ku da kuma Shugabancin kungiya na kasa muna tare da ku a wannan mawuyacin lokaci. Yajin aikin namu halastacce ne kuma yana bin kowane tsarin da ya dace.

"Saboda haka, muna tsaye kan manufar "Babu albashi, Babu aiki". Wannan tsarin raba kai da mulki na Gwamnati ba zai yi aiki ba.

"Ku kwan da sanin cewa za mu fito da kyau, da karfi tare da kudaden da aka biya kafin ko kuma lokacin dawowa aiki. Mu kasance kai a hade, kungiyarmu ke bamu karfi."

Shugaban kungiyar ya kuma yi barazanar cewa mambobin kungiyar za su tabbatar da cewa sun ji da duk wanda ke adawa da bukatar ma’aikata a 2023.

Ya ce:

“Ina kira ga daukacin ma’aikata a Najeriya da ma’aikatanmu na NAAT da su tashi tsaye wajen ganin mun taka rawar gani a duk harkokin siyasa tare da daukar makomarmu a hannunmu."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN