Sokoto: ICPC ta tilasta wa ɗan majalisa rabar da kayan tallafi da ya ɓoye a gida

 


Bayan Hukumar Yaki da Rashawa Mai Zaman Kanta, ICPC ta shiga lamarin, dan majalisa mai wakiltar mazabar Kebbe da Tambuwal, Bala Kokani ya rarraba babura da kekunan dinkin da ya boye a gidansa da ke Sokoto, Daily Nigerian ta rahoto.

Hakan ya biyo bayan yadda wani mai fallasa ya kai karar dan majalisar ga ICPC, inda ya sanar da hukumar yadda ya ki rarraba kayan sana’ar wanda hakan na cikin ayyukan da ya dace ya yi wa mazabar.

Kayan, kamar yadda mai korafin ya ce, an tanade su ne don bunkasa tattalin arziki ga mutanen mazabar, wadanda ya kamata ya raba wa jama’a don yaki da rashin aikin yi da kuma bunkasa sana’o’in masa kananun jari tare da koyon sana’a ga marasa su.

Ya so adana kayan ne don siyan kuri’u lokacin zaben 2023

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, mai korafi ya ce, dan majalisar ya yi amfani da damar ne wurin dankare kayan aikin a gidansa da ke jihar don ya rarraba kayan lokacin zaben 2023, don siyan kuri’un jama’a.

Hakan ya sa hukumar ICPC ta zabura ta fara aiki, ta bibiyi gidan dan majalisa inda ta gano duk kayan da mai karar ya sanar da ita.

Bayan ya samun labarin hukumar ta gano halin da ake ciki, Kokani, dan majalisa karkashin jam’iyyar APC ya nemi kariya daga shugabancin majalisar don gudun a tozarta shi.

ICPC ta amince da cewa ba za ta tozarta dan majalisar ba a gaban jama’a, amma ta tilasta shi rarraba kayan ga mutane cikin gaggawa ko kuma ta hukunta shi.

A ranar 20 ga watan Mayun 2022, Daily Nigerian ta samu takardar da Kokani ya amince da bin sharuddan da hukumar ta kafa masa.

Ya sanar da hukumar rana da lokacin da zai raba kayan

Kamar yadda takarda ta zo:

“Na rubuto wannan takardar ne don in sanar da hukumar cewa zan rarraba kayan ga mutanen yankina a ranar Talata, 24 ga watan Mayun 2022 da misalin karfe 12 na rana a garin Kebbe, hedkwatar karamar hukumar Kebbe da ke jihar Sokoto.”

Da farko dan majalisar don gudun gwamnatin tarayya ta shiga, ya siya duk kayan rabon inda ya killace su har sai zaben 2023 don ya siya kuri’un mutane.

Ana zarginsa ne bayan ganin yadda ake ta zaben fidda gwanin babbar jam’iyyar ana siyan kuri’u daga hannun wakilan jam’iyya ta hanyar ba su kudade da tsadaddun abubuwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN